Sauyin da aka gani daga gwamnatin Donald Trump ya bayyana a fili a ranar Litinin, yayin da Amurka da Rasha suka yi matsaya ɗaya a taron Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
Kasashen biyu sun ƙi amincewa da wani daftarin ƙasashen Turai da ke yin tir da Rasha tare da goyon bayan Ukraine, duk da cewa babban zauren MDD ya amince da shi. Sai dai daga bisani, sun amince da kudirin da Amurka ta gabatar, wanda ke kira da a kawo ƙarshen yaƙin ba tare da sukar Rasha ba.
Birtaniya da Faransa sun ƙaurace wa kaɗa ƙuri’a kan wannan kudiri, yayin da shugabanninsu ke shirin ganawa da Trump a mako mai zuwa don tattauna batun zaman lafiya.
