Jam’iyyar NNPP tsagin Sanata Mas’ud Jibrin El- Doguwa ta ce har yanzu Sanata kawu Sumaila da Aliyu Sani Madakin Gidi da Sani Rogo da kuna Kabiru Alasan Rurum Yayanta ne na halali.
Jibrin El-Doguwa ya kuma ce uwar Jam’iyyar NNPP ta kasa ce ta tabbatar da shi a matsayin shugabanta na Kano a domin haka dakatarwar da Hasim Dungurawa dake tsagin kwankwasiyya ya yiwa membobin su bai yuwuba.
A cewarsa akwai tsare tsaren da akebi wajen Dakatar da duk wani dan Jam’iyya idan ya aikata laifi.
El- Doguwa ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a yau.
Kazalika ya ce, jam’iyyar ta dade da Dakatar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.
