Jam’iyyar NNPP a nan Kano ta dakatar da sanatan Kano ta Kudu Abdurrahman Kawu Sumaila sakamakon zargin sa da cin amanar jam’iyya.
Haka zalika jam’iyyar ta dakatar da wasu yan majalisar wakilai uku da suka hadar da Ali Madakin Gini dake wakiltar karamar hukumar Dala da da Kabiru Alhassan Rurum dake wakiltar kananan hukumomin Rano da Kibiya sai kuma Sani Rogo dake wakiltar kananan hukumomin Rogo da Karaye.
Hakan na zuwa ne lokacin da shugaban jam’iyyar NNPP a nan Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, ke ganawa da manema labarai a yau.
Kazalika ya ce dukkan wadan da aka dakatar din an zabesu ne a karkashin jam’iyyar NNPP amma daga baya sai suka samusu ya yiwa jam’iyyar zagon kasa.
Ya kuma zargi sanatan Kano ta Kudu Kawu Sumaila da kin gayyatar yayan jam’iyyar lokacin da zai kaddamar da ayyuka tare sai ya gayyacin yan jam’iyyar Adawa.
