Hukumar Kula da Farashin Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta sanar da sabbin dokoki da ke tanadar da tarar naira dubu 100 zuwa 300 ga masu yin cuta a mitar wutar lantarki. Wannan matakin ya biyo bayan sabunta dokokin hukumar da aka yi don hukunta masu yin amfani da mitar lantarki ba bisa ka’ida ba.
Dokar mai lamba NERC/REG/41/2017, wadda ta fara aiki a ranar 22 ga Janairu, 2025, ta tanadi cewa masu amfani da mita mai layi daya (single-phase) za su biya tarar naira dubu 100 idan sun aikata laifi na farko, sannan naira dubu 150 idan sun sake aikata laifi na biyu. Ga masu amfani da mita mai layi uku (three-phase), za su biya tarar naira dubu 200 idan sun aikata laifi na farko, sannan naira dubu 300 idan sun sake aikata laifi na biyu.
Wadannan matakan sun kasance ne don dakile ayyukan da suka hada da jirkita mitar wutar lantarki ko amfani da wuta ba tare da siyan kati ba, domin tabbatar da adalci ga duk masu amfani da wutar lantarki a Najeriya.
