Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ya saka hannu kan wasu dokoki guda Uku da suka hadar da Dokar Samarda hukumar Kano Metropolitan Area Transport Authority, da Kano Centre for Disease Control and prevention law 2025 sai kuma Kano State Security Neighborhood watch law 2025.
Da yake jawabi cikin harshen turanci bayan saka hannu a dokokin yayin zaman majalisar zartarwar Gwamnatin Kano karo na Ashirin da Biyar da ya gudana yau Talata 18 ga watan Fabrairun shekarar 2025.
Gwamna Abba Kabir Yusif,ya ce samar da dokokin zai Ingantar Harkokin Lafiya, Tsaro da Sufuri dan habbaka tatalin arziki jihar Kano.
Gwamnan ya kuma bukaci al’ummar jihar Kano da su cigaba da baiwa gwanati hadinkai wajen samar da ayyukan cigaba.
