An sanar da rasuwar Edwin Clark, jagoran kungiyar al’ummar Neja Delta (PANDEF), wanda ya rasu yana da shekaru 97. Clark ya taba rike mukamin kwamishinan yada labarai na gwamnatin tarayya. Sanarwar rasuwarsa ta fito ne daga Farfesa C. C. Clark, daya daga cikin iyalansa, wanda ya bayyana cewa Clark ya rasu a daren jiya Litinin.
Rasuwar Clark ta biyo bayan mutuwar jagoran kungiyar Yarbawa ta Afenifere, Ayo Adebanjo, wanda ya rasu kwanaki kadan da suka gabata yana da shekaru 96.
Edwin Clark ya kasance fitaccen dan siyasa kuma mai fafutukar kare hakkin al’ummar Neja Delta. A tsawon rayuwarsa, ya yi gwagwarmaya wajen ganin an samu adalci da ci gaba a yankin kudu maso kudancin Najeriya.
Rasuwarsa babban rashi ne ga al’ummar Neja Delta da Najeriya baki daya.
