Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (Customs) ta cafke wasu bindigu da alburusai da aka shigo da su Najeriya ta jihar Legas ba bisa ka’ida ba.
Duk da cewa ba a bayyana adadin makaman da aka kama ba, hakan ya kara dagula damuwa kan fasa kwaurin makamai da ke barazana ga tsaron kasa.
Shugaban hukumar, Adewale Adeniyi, ya ziyarci Legas domin karin bayani ga manema labarai kan yadda aka samu nasarar cafke makaman da kuma matakan da za a dauka. Ana sa ran bayaninsa zai bayyana asalin makaman da irin matakin da hukumomi za su dauka kan lamarin.
