Kamfanin mai na NNPCL ya rage farashin litar fetur daga N960 zuwa N945, bisa umarnin da ya bai wa gidajen man sa a yau Alhamis.
Sai dai wasu masu ababen hawa sun bayyana cewa ragin bai da wani tasiri, domin ba zai kawo saukin rayuwa ba.
A halin yanzu, gidajen mai na ‘yan kasuwa na siyar da fetur tsakanin N960 zuwa N970 kan kowacce lita. Kamfanin MRS kuwa ya rage farashin zuwa N925 a Legas, yayin da a arewacin Najeriya yake siyar da lita akan N955.
