Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta kama wani magatakardan babbar kotu, mataimakinsa Sheriff mai ritaya, lauyoyi uku, da wasu jami’an tsaro 10 bisa zarginsu da hannu a badakalar kudi sama da Naira biliyan 20.
Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin-Gado, ya bayyana hakan a yau Alhamis yayin wani taron manema labarai a hedikwatar PCACC.
Ya ce sun bankado wata kungiya da ke aikata laifuka, musamman kwace filayen jama’a, tare da hadin gwiwar lauyoyi, ma’aikatan kotuna, jami’an rajistar filaye, da jami’an tsaro. Muhuyi ya bayyana damuwarsa kan yadda ake taimaka wa haramtattun ayyuka a jihar, yana mai cewa ana daukar matakin hukunta wadanda aka kama.
