Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) dake Bauchi ta ba dalibanta damar yin amfani da tukunyar Gas mai nauyin 3kg don girki, bayan da ta haramta amfani da Gas gaba daya a baya saboda tsoron gobara. Shugaban kula da al’amuran dalibai, Farfesa Sa’id Umar, ya bayyana hakan yayin wayar da kan sabbin dalibai, inda ya gargadi masu karya doka da hukunci. Hukumar kashe gobara ta jihar Bauchi ta jaddada cewa kaso 90 na gobara na faruwa ne sakamakon sakaci.
