Gwamnatin jihar Kano ta ce a shirye take ta rungumi sabbin dabarun Noma na zamani da zasu taimakawa manoma wajen bunkasa Tattalin arziki da rage matsalar sauyin Yanayi.
Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano Dakta Dahiru Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa da tuntubar masu ruwa da tsaki ciki harda manoma da masana kan shirin dabarun Noma dake Inganta muhalli na TOURBA a Najeriya.
Dakta Dahiru Hashim ya kuma ce kirkiro da sabbin dabarun Noma zai sa a rinka samun wadatattun kayan abinci.
A cewar sa wannan dumamar yanayi da ake samu da yake sanya samun karancin amfani a kowacce damu zai magance matsalar.
Ya kuma ce samar da amfanin gona daban daban a guri daya zai saka a rage barnatar da takin da ake a gonaki.
A nasa jawabin babban malamani gona na Tourba a nan Najeriya Malam Yusuf Ali Bello ya ce sun shirya taron ne dan nunawa manoma yadda ake hada amfanin gona a waje guda.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin Noma a matakai daban daban da shugabannin al’umma inda aka wayar da kai kan yadda xa a samar da dabarun noma
