Wani jami’in rundunar ‘yan sanda mai suna Dogara Akolo-Moses ya kashe kansa ta hanyar bindige kansa a ofishin ‘yan sanda na yankin Mada, karamar hukumar Nasarawa Eggon.
Shaidu sun bayyana cewa Akolo-Moses ya shiga ɗaki inda ya harbe kansa, lamarin da ya janyo hankalin mutane bayan jin karar harbin. An same shi cikin jini tare da bindigarsa a gefe, kuma har yanzu ba a gano dalilin aikata hakan ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da bincike kan musabbabin wannan abin al’ajabi.
