Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirin kashe Naira biliyan 2.5 domin gudanar da auren zawarawa a duk fadin kananun hukumomi 44 na jihar a shekarar 2025.
Kwamishinan kasafin kudin jihar, Musa Shanono, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani ga manema labarai kan abubuwan da kasafin kudin shekarar 2025 ya kunsa, bayan amincewar majalisar dokoki ta jihar.
Haka nan, gwamantin za ta kashe Naira biliyan 1 domin ciyar da al’umma a watan Azumin Ramadan mai zuwa.
Source: Dailynews24.ng.com/hausa
By Rahma kabir
