Wani direban da ya sha giya ya murkushe sojoji hudu har lahira tare da jikkata wasu yayin da suke yin atisaye a barikin Myoung, dake Yaba, Lagos, a safiyar Juma’a. Wata shaidar gani da ido, Priscilla, ta ce mutane uku ne ke cikin wata mota kirar Toyota, suna gudun wuce sa’a, inda suka bi ta kan sojojin. Rahotanni sun tabbatar da cewa direban ya rasa hayyacinsa sakamakon shan giya kafin afkuwar lamarin.
source:Dailynews24.ng.com/hausa
By:
