Kocin ƙasar Spain, Luis de la Fuente, ya bayyana cewa matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, na kan hanyar zama ɗaya daga cikin manyan fitattun ’yan wasan ƙwallon ƙafa a tarihi.
De la Fuente ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ƙwararren mai sharhin harkokin musayar ’yan wasa, Fabrizio Romano, ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi.
Kocin na Spain ya ce Yamal yana “kan hanyar zama cikakken gwarzon ƙwallo na tarihi”, abin da ke nuna irin babban darajar da yake bai wa matashin ɗan wasan mai shekaru ƙalilan.
De la Fuente ya kuma bayyana cewa idan har Yamal ne kaɗai daga cikin ’yan wasan Spain da ke cikin jerin masu neman lashe kyautar Ballon d’Or, to zai ɗauke shi a matsayin ɗan takarar da ya fi dacewa da ƙasar.
Ya ce, idan Yamal ne kaɗai ɗan Spain da ke cikin takarar Ballon d’Or, zai ce shi ne mafi cancanta.
Sai dai kocin ya jaddada cewa akwai wasu ’yan wasan Spain da dama da suka cancanci yabo da karramawa, yana mai cewa ba ya son ya raina ƙoƙarin sauran ’yan wasan ƙasar.
Ya ce: “Akwai wasu daga cikin ’yan wasanmu kuma ina girmama su.”
Lamine Yamal ya zama ɗaya daga cikin matasan ’yan wasan da suka fi jan hankalin duniya, musamman saboda irin rawar da yake takawa a Barcelona da kuma tawagar ƙasar Spain.
Kokarinsa a filin wasa ya ci gaba da jawo yabo, yayin da ake ƙara kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin matasan da za su iya taka muhimmiyar rawa a tarihin ƙwallon ƙafa a shekaru masu zuwa.
Kalaman De la Fuente sun ƙara nuna irin babban fata da tawagar Spain ke da shi kan makomar Yamal, musamman yadda yake ci gaba da haɓaka kwarewarsa tun yana ƙaramin ɗan wasa.
