Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Turai, UEFA, ta tabbatar da cewa ɗan wasan Portugal, Rafael Leão, zai sanya rigar lamba 7 a wasannin UEFA Nations League guda biyu na ƙasar, bayan Cristiano Ronaldo ya fice daga sansanin tawagar.
Leão, wanda aka fi saninsa da sanya lamba 17 a tawagar Portugal, zai bayyana da lamba 7 a jerin ’yan wasan da aka gabatar wa UEFA domin wasan da Portugal za ta yi da Denmark a Copenhagen a ranar Alhamis, da kuyin lambar ya biyo bayan ficewar Ronaldo daga sansanin tawagar Portugal.
Sabon Ɗan Wasa Ya Karɓi Lambar Leão
Sabon ɗan wasan da aka kira zuwa tawagar Portugal, Fábio Silva, shi ne zai sanya lamba 17, wadda a baya Leão ke amfani da ita.
An bayyana cewa wannan sauyin ya zama dole ne saboda dokokin UEFA Nationsh League, waɗanda suka tanadi cewa ’yan wasa 23 da za su kasance cikin jerin ’yan wasan da za su buga wasa dole ne su sanya lambobi daga 1 zuwa 23 ba tare da wani gibi ba.
Saboda haka, bayan Ronaldo ya fice daga tawagar, an sake tsara lambobin ’yan wasan domin cika ƙa’idar UEFA.
Ronaldo Ya Fice Daga Sansanin Portugal
Cristiano Ronaldo ya bar sansanin tawagar Portugal a ranar Laraba, bayan bai buga wasan da Portugal ta doke Norway da ci 2-1 a ranar Lahadi ba, inda ya kasance cikin ’yan wasan da ba a yi amfani da su ba.
Ronaldo, mai shekaru 41, ya fara wasan da ya gabata, wanda Portugal ta doke Wales da ci 1-0. Wannan wasan shi ne na farko da sabon kocin Portugal, Jorge Jesus, ya jagoranta.
A halin yanzu, Portugal ce ke jagorantar rukunin A4 bayan samun nasara a wasanni biyu.
Tawagar za ta ziyarci Parken Stadium domin karawa da Denmark, kafin daga bisani ta koma gida domin karɓar Norway a Estádio do Dragão ranar Lahadi.
