Kamfanin rarraba wutar lantarki na Ikeja Electric Plc ya fara mayar wa wasu kwastomominsa kuɗin da suka biya domin samun mita ƙarƙashin shirin Meter Asset Provider (MAP).
Kamfanin ya bayyana hakan ne yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na watan Satumba, wanda ake gudanarwa duk wata domin sanar da kwastomomi abubuwan da suka shafi ayyukansa tare da amsa tambayoyi da korafe-korafensu.
Ikeja Electric ta ce kwastomomin da suka cancanci samun kuɗin za su karɓi maida kuɗin ne ta hanyar ƙara musu adadin kuɗin a asusun da suke amfani da shi wajen sayen wutar lantarki, cikin wa’adin da aka amince da shi.
Yadda Za a Bibiyi Maida Kuɗin
Kamfanin ya bayyana cewa kwastomomi za su iya bibiyar matsayin maida kuɗinsu ta hanyar refund dashboard na intanet, inda za su shigar da lambar mitarsu ko lambar asusunsu.
Dashboard ɗin zai nuna bayanai kamar kuɗin da aka biya wajen sayen mita, adadin maida kuɗin da aka kammala, adadin kuɗin da ake mayarwa a kowane wata, jimillar kuɗin da aka mayar da kuma ranar da aka yi maida kuɗi na ƙarshe.
Kwastomomi za su kuma iya samun refund token ɗinsu ta wannan hanyar, inda za a aika musu da token ɗin zuwa lambar waya ko adireshin imel da suka yi rajista da kamfanin.
Ikeja Electric ta shawarci kwastomomin da ke buƙatar ƙarin bayani ko kuma son yin ƙorafi kan maida kuɗin da su yi amfani da hanyoyin korafi na hukuma ko kuma su ziyarci ofishin kamfanin mafi kusa.
Gargadi Kan Amfani da Masu Gyaran Wuta Ba Bisa Ka’ida Ba
A yayin taron, kamfanin ya kuma bayyana damuwarsa kan ƙara yawan haɗurran da ke tattare da amfani da ma’aikatan lantarki marasa izini.
Shugaban Sashen Inganci, Lafiya, Tsaro da Muhalli na kamfanin, Olaniyi Olayiwola, ya ce wasu sabbin abubuwan da suka faru sakamakon ayyukan lantarki marasa aminci sun jawo asarar rayuka.
Ya gargadi kwastomomi da kada su bari mutanen da ba su cancanta ba su hau kan turakun Ikeja Electric, su yi aiki a kan layukan wuta, su tsoma baki cikin na’urorin lantarki ko kuma su haɗa wutar lantarki ba bisa ƙa’ida ba.
Olayiwola ya buƙaci jama’a da su kai rahoton duk wani aiki mai hatsari da suka gani a kusa da kayayyakin kamfanin, maimakon su tunkari mutanen da ke gudanar da aikin.
Ya kuma yi kira ga mazauna unguwanni da al’ummomi da su nisanta kansu daga manyan layukan wutar lantarki masu ƙarfin gaske, yana mai cewa mamaye wuraren da aka tanada don kayayyakin lantarki da rashin isasshen tazara daga layukan wuta na daga cikin matsalolin tsaro da ake fuskanta.
Shi ma Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na Ikeja Electric, Kingsley Okotie, ya ƙarfafa wa kwastomomi gwiwa da su nemi bayanai da kuma gabatar da korafe-korafensu ta hanyoyin sadarwa da kamfanin ya amince da su.
Ya ce ci gaba da tattaunawar kamfanin da kwastomomi na da nufin tabbatar da cewa jama’a suna samun bayanan da suka dace, musamman kan tsaro, samun taimako da kuma yadda za a warwarekorafe-korafe.