Gwamnan Jihar Niger, Umar Bago, ya sanya dokar hana fita na tsawon sa’o’i 24 a fadin jihar, biyo bayan zanga-zanga da lalata kadarori da aka alakanta da mutuwar wasu da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne da ke tsare a hannun Rundunar NSCDC.
Gwamnan ya sanar da matakin ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Juma’a, inda ya ce dokar za ta fara aiki nan take bayan kammala sallar Juma’a.
Bago ya ce gwamnati ta dauki matakin ne domin dawo da zaman lafiya, bayan da masu zanga-zangar suka lalata wasu kadarorin gwamnati, banki, ofisoshin jam’iyyu da kuma wasu wuraren kasuwanci na jama’a.
Ya bayyana cewa tashin hankalin ya sa wasu masu aikata barna suka mamaye tituna, lamarin da ya sa gwamnati ta ga bukatar takaita zirga-zirga domin hana ci gaba da lalata kadarori.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankula, su kuma yi hakuri yayin da hukumomi ke kokarin dawo da zaman lafiya.
Dokar hana fita ta biyo bayan mutuwar mutane 37 da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne, wadanda aka kama a yankin Wushishi/Lukoto a ranakun 15 da 16 ga Satumba, 2026, a wani samame da hukumomi suka gudanar kan ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Gwamnatin jihar ta ce ana gudanar da binciken likitanci, na gawarwaki da kuma na kimiyyar forensics domin gano ainihin musabbabin mutuwar. Har yanzu ba a tabbatar da dalilin mutuwar ba.
Hukumar NSCDC ta kafa kwamitin bincike domin duba halin da wadanda ake zargin suke ciki lokacin da aka kama su, yadda suka kasance a tsare, yanayin wurin tsarewar da kuma irin kulawar lafiya da aka ba su.
Haka kuma, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Niger, Suberu Siyaka Aniviye, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta kare duk wanda aka samu da hannu a lamarin ba, amma ta bukaci jama’a su jira sakamakon binciken kafin a yanke hukunci kan wanda ke da alhaki.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a 2027, Atiku Abubakar, shi ma ya bukaci a tabbatar da adalci da rike duk wanda bincike ya tabbatar da cewa yana da alhaki kan mutuwar mutanen.
A halin yanzu, hukumomi na ci gaba da bincike domin gano abin da ya haddasa mutuwar mutanen da kuma tabbatar da alhakin duk wanda bincike ya nuna yan8a da hannu.
